Dandalin Siyasa

Dandalin Siyasa

Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
00:00
00:00

Σύνοψη επεισοδίου

Shirin ‘Dandalin Siyasa’ tare da Michael Kuduson a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya kan shirin samar da rangwamen farashin man fetur na tsawon kwanaki 30, da martanin ’yan adawa. Sannan za mu waiwayi hukuncin Kotun Ƙoli da kuma matsayin Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, kan jam’iyyun siyasar da suka saɓa ƙa’idojin miƙa rajistar mambobinsu, da dai sauran batutuwan da muka tanadar muku a shirin. A daidai lokacin da ƴan Najeriya ke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, musamman farashin man fetur da sufuri, gwamnatin ƙasar ta sanar da wani mataki na rage nauyin da ke kan al’umma. Gwamnatin ta ce za a sayar da man fetur bisa rangwame a gidajen mai na kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC, na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu jigilar fasinjoji fifiko. Sai dai mataki bai burge ƴan adawa ba, domin kuwa sun mayar da martani, inda suke ke tambaya ko rangwamen na ɗan lokaci zai iya magance matsalolin da suka shafi tsadar rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakke shirin.

Επεισόδια

165-

Shirin ragin kuɗin man fetur na wata 1 ya janyo cece-kuce a Najeriya

10 Οκτ 2026
164-

Jawabin Tinubu na cika shekaru 66 da samun ƴancin kan Najeriya ya bar baya da ƙura

Shirin ‘Dandalin Siyasa’ na wannan mako, ya maida hankali ne kan cikar Najeriya shekaru 66 da samun ƴancin kai, kuma yayin da ake bikin wannan rana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan ƙasar jawabi inda ya jaddada nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta ce ta samu a fannin tattalin arziki, tare da bayyana fatansa na ganin ƙasar ta samu ƙarin wadata. Sai dai shugaban bai yi magana kan matsalar tsaro da ke ci gaba da ta zame wa wasu sassan ƙasar ƙarfen ƙafa ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.............

03 Οκτ 2026
163-

A Najeriya shirin yaƙin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki

Shirin na wannan makon tare da Michael Kuduson, ya yi nazari ne akan yadda a Najeriya yakin neman zaben 2027 ya shiga wani sabon mataki, bayan fara yakin neman zaben kujerun gwamna da ’yan majalisun jihohi a hukumance, inda Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta kuma tunatar da ’yan takara da jam’iyyun siyasa cewa dole ne su gudanar da yakin neman zabe bisa tanade-tanaden doka.

12 Σεπ 2026
162-

INEC na duba yiwuwar gudanar da zaɓen gwaji na shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027

Shirin na wannan makon, ya karkata ne kan yadda jam'iyyun siyasa ke ƙoƙarin cimma matsaya game da yadda za su tunkari zaɓen 2027, daidai lokacin da Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC, na duba yiwuwar gudanar da zaɓen gwaji amma, na shugaban ƙasa, domin tantance shirye-shiryen tsarin zaɓen na baɗi. Wannan na zuwa ne, yayin da cikin makon jiya, aka jiyo Shugaba Bola Tinubu na bayyana cewa ɓangaren Arewacin ƙasar ne ya fi cin gajiyar wasu daga cikin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ƙaddamar, abin da ya fuskanci suka da caccaka daga masu ruwa da tsaki da ƙungiyoyin fararen hula. A gefe guda kuma, batun yadda ake tallafa wa jama'a a lokutan matsin tattalin arziki na cigaba da zama wani batu na siyasa, inda Ministan Tsaro ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su daina raba babura a matsayin tallafin gaggawa ga jama'a, yana mai neman a mayar da hankali kan hanyoyin da za su samar da mafita mai ɗorewa. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.

05 Σεπ 2026
161-

Ƴan adawa sun kaɗa hantar jam'iyar APC mai mulki a Najeriya

Yayin da aka kaɗa gangar siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027 da ke kara kusantowa, ƴan siyasa na ci gaba da gabatar da manufofi da alƙawuran da suke cewa za su inganta rayuwar ƴan Najeriya. A wannan makon, batun tallafin man fetur, sake bude iyakokin ƙasa da matsalar tsaro sun sake zama wasu daga cikin muhimman batutuwan da ƴan adawa ke amfani da su wajen ƙalubalantar gwamnati. Ku lasha alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson...........

29 Αύγ 2026